MU HADU A LITTAFI NA GABA

MU HADU A LITTAFI NA GABA


Wani mai share cikin jirgin sama ne mai karambani bayan ya shiga jirgi don yin goge-goge kamar yadda ya saba, sai ya tarar da wani littafi mai taken: “YADDA AKE KOYON TUkIN JIRGIN SAMA A SAUkAkE.”

Yana bude shafin farko sai ya ga an rubutu “Idan aka danna, kaza da kaza, za a tayar da injin jirgi. Sai ya danna, injin jirgi ya fara aiki. Sai ya bude shafi na gaba, nan kuma aka rubuta “Idan aka danna kaza da kaza, jirgi zai fara tafiya, nan ma ya danna, jirgi ya fara tafiya.

Can da ya bude shafi na gaba, sai ya ga an rubutu “Idan aka danna kaza da kaza jirgi zai yi sama, nan ma ya danna jirgi ya tashi sama da shi. Da ya bude shafi na gaba, sai idonsa ya raina fata don ya ga an rubuta “Don jin yadda jirgi ke sauka sai a biyo mu a littafi na gaba!”
Post a Comment (0)