1. Jinin Biƙi Da Hukunce-Hukuncensa

1. Jinin Biƙi Da Hukunce-Hukuncensa.
.


Jinin biƙi shine jinin da yake zubowa daga mahaifa saboda haihuwa da kuma bayanta. Shi ne sauran jini ne da yake tsare a cikin mahaifa lokacin da mace take da ciki, Idan ta haihu sai jinin ya rika fita kadan-kadan. Jinin da mace take gani kafin haihuwa idan dai akwai alamar haihuwa tare shi, to shi ma jinin biki ne. Malaman Fiqhu sun kayyade shi da kwana biyu ko uku kafin haihuwar. Amma a yawaici farkon zubarsa yana zuwa ne tare da haihuwa. Kuma haihuwar da ake nufi itace wadda halittar mutum take bayyana ga abinda aka haifa. Mafi ƙarancin lokacin da halittar mutum take bayyana shi ne kwana 81, a galibi kuma wata 3 ne. Wadda ta yi ɓari kafin Wannan lokacin, kuma aka sami jini, to ba za ta ɗauki Wannan jinin akan komai ba; ba za ta bar sallah da azumi ba Saboda shi, domin jini ne na rashin lafiya. Hukuncin ta kamar hukuncin mace ce mai jinin rashin lafiya.
.
Mafi tsawon lokacin jinin biƙi kwana 40 ne daga ranar haihuwa, ko kafin ta da kwana 2 ko 3, kamar yadda ya gabata. Dalili hadisin Ummu Salama (r.a) ta ce: “Masu jinin biƙi sun kasance suna zama kwana arba'in a zamanin manzon Allah (ﷺ)." Tirmidzy da waninsa suka ruwaito shi.
.
Dukkan malamai sun haɗu akan Wannan, kamar yadda Tirmidzy da waninsa suka faɗa. Idan ta ga tsarki kafin kwana arba'in din, wato Idan jinin ya yanke, to sai ta yi wanka, ta yi sallah.
.

Babu iyaka ga mafi karancinsa, domin babu abin da ya zo akan haka.


Idan ta cika kwana arba'in kuma jinin be yanke ba, to Idan lokacin ya dace da lokacin al'adarta ta haila, to jinin haila ne. Idan kuma be dace da lokacin al'adar hailarta ba, kuma ya ci gaba bai yanke ba, to jinin rashin lafiya ne. Ba za ta bar ibada ba Saboda shi, Idan dai ta cika kwana arba'in din. Idan kuma ya zarce kwana arba'in, amma bai ci gaba ba, kuma bai dace da al'adar haila ba, to anan akwai saɓani tsakanin malamai.
.

Allah Ya sa mu dace. 
.

*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*Ansar.*

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*
Post a Comment (0)