BASHI BA YA SARAYAR DA ZAKKAR NOMA

BASHI BA YA SARAYAR DA ZAKKAR NOMA 


:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum Wa rahmatullah, Akramakallah ana bina bashi, yanzu na girbe amfanin gona, shin zan cire wanda zan siyar na biya bashin kafin na fitar da zakka ne ko kuwa zan fitar da zakka ne da farko? Allah ya dada imani.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam
Za ka fara fitar da Zakka ne, saboda bashi ba ya tasiri a zakkar noma, ana kallon abin da ka samu ne kawai, mutukar ya Kai nisabi za ka fitar da zakka ko da ana binka bashi.

Inda tsabar kuɗi ne sai ka fara biyan bashi kafin ka bada Zakka, saidai lamarin ba haka yake ba a Zakkar noma.

Allah ne mafi sani 

Don neman Karin bayani duba Sharhin Alpiyatul Usul shafi na 294.

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

1 Comments

  1. Menene hukucin afanidabuduruwar da baba tayace yabaka ita bayan bakuyi aureba

    ReplyDelete
Post a Comment