TAURIN BASHIN MAWADACI ZALUNCI NE

TAURIN BASHIN MAWADACI ZALUNCI NE.


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum, akramakallahu tambaya ta akan bashi ne, akramakallah ya muslunci ya tsara akan wadannan ka ke bi bashi amma sun hanaka kuma suna da kuɗin. Wace azaba Allah ya tanadarwa wadan da basa biyan bashi. nagode daga 
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam To dan'uwa taurin bashi mawadaci zalunci ne yana halatta mutuncinsa da yi masa ukuba kamar yadda hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito a Musnad a lamba ta: 17945, kuma Ibnu Hajar ya kyautata ya tabbabtar da hakan.

Duk wanda ya karbi bashin mutum da niyyar zai mayar masa, Allah zai taimaka masa wajan mayarwa.

Ya halatta ka kai wanda kake bi bashi kotu, don ta amsar maka hakkinka, mutukar ka tabbatar yana da shi amma ya hana ka, saboda hadisin da ya gabata.
In har aka tabbatar da cewa rashin kuɗi ne ya hana shi biya, ya wajaba a jira har ya samu, kamar yadda aya ta: 280 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan.

Biyan bashi akan lokaci yana da mutukar muhimmanci, saboda wanke tukunya don gobe yana saukake girki.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍️

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)