WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA

WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA.
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum.
Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta yadda ba za ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam ko akwai wasu lokuta ne da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila ?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar a saki mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa "Idan za ku saki mata to Ku sake su a farkon iddarsu) ma'ana a tsarkin da ba ku take su ba, Addalak aya ta : (1) saidai akwai wurare guda hudu da ya halattta a saki mace mai haila :

1.Idan sakin ya kasance kafin ya Kaɗaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.

2. Idan ta yi hailar ne tana da ciki.

3. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi s.a.w. bai tambayi matar Thabit ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul'i, kamar yadda Bhukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 5273.

4. Idan watanni huɗu suka cika a lokacin ila'i, to ko da tana haila zai iya sakinta.

Don neman karin bayani duba : Dima'uddaabi'iy ya shafi na :33

In banda waɗannan wurare, to bai halatta a saki mai haila ba, kuma yin har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu malaman.

Allah ne mafi sani.
*Dr.Jamilu Zarawa*

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana.
Post a Comment (0)