JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 09

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 09


ABUBUWAN DA SUKA FARU A HANYA
Mun fara maganar Manna da Salwa don warware matsalar mahallin da abin ya faru acan, wato duk wadannan falala da banu Isra'ila suka samu ba a Sina ba ne inda suka kwashe shekara 40 suna watangariri, a kan hanyarsu ne ta barin Masar zuwa bigire mai tsarki da aka yi musu alqawari bayan sun bar Masar, Allah SW ya sauwaqe musu komai kamar yadda muka karanta a baya, sai dai kuma daga cikin wadanda suka biyo Musa AS ba muminai kadai ba akwai ma kafurai, kafuran sun biyo shi ne don tsoron azabar Fir'auna, domin azabtar da su da aka riqa yi ba don sun qi bautar Fir'aunan ne kawai ba har da qabilanci ma.
.
Tun bayan rasuwar Yusuf AS a qasar Masar banu Isra'ila suka shiga halin qaqa-nikayi har zuwa lokacin Musa AS, Allah SW yake cewa {فَمَا آمَنَ لِمُوسَى إِلَّا ذُرِّيَّةٌ مِنْ قَوْمِهِ عَلَى خَوْفٍ مِنْ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِمْ أَنْ يَفْتِنَهُمْ} (Ba wasu ne suka yi imani da Musa ba face wasu jama'a daga cikin mutanensa saboda tsoron Fir'auna da mutanensa kar ya fitine su) suratu Yunus85, don haka suna tsallakowa teku suka ce masa "Mu fa ba za mu miqa maka wuya ba sai mun ga Allan baro-baro!"
.
Duk da cewa fa duk ayoyin da Musa AS ya nuna wa Fir'auna da mutanensa a kan idanunsu ne, cikin sanyin zuciya suka ce {لَنْ نُؤْمِنَ لَكَ حَتَّى نَرَى اللَّهَ جَهْرَةً فَأَخَذَتْكُمْ الصَّاعِقَةُ وَأَنْتُمْ تَنظُرُونَ * ثُمَّ بَعَثْنَاكُمْ مِنْ بَعْدِ مَوْتِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ} (Ba za mu taba yarda da kai ba sai mun ga Allah ido da ido, nan take wata tsawa ta abka muku kuna kallo. Sai kuma muka sake tashinku bayan kun mutu don dai ku yi godiya) Baqara 55-56, to ko wannan ya ishi banu Isra'ila su hankalta su tsaya wurin kadaita Allah.
.
Da ma Allah SW ya fadi halayensu, wadanda suka biyo bayan na zamanin Annabi Musa AS ma ba sa hana mabarnata yin komai, sai su zauna tare da su, Allah SW ya ce {وَجَاوَزْنَا بِبَنِي إِسْرَائِيلَ الْبَحْرَ فَأَتَوْا عَلَى قَوْمٍ يَعْكُفُونَ عَلَى أَصْنَامٍ لَهُمْ قَالُوا يَا مُوسَى اجْعَلْ لَنَا إِلَهًا كَمَا لَهُمْ ءَالِهَةٌ قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ} (Muka hayar da banu Isra'ila teku, da suka zo wurin wasu masu gurfana a gaban gumakansu sai suka ce "Musa mu ma ka sanya mana wani abin bauta mana kamar yadda suke da shi" ya ce "Haqiqa kun yi aikin rashin sani") A'araf 138. Har sun manta da cewa abinda ya halakar da Fir'auna da mutanensa rashin tauhidi ne.
.
Haka dai Annani Musa da banu Isra'ila suka yi ta tafiya har suka isa wurin da Allah SW ya umurce su { اهْبِطُوا مِصْرًا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلْتُمْ } (Ku sauka wata qasa za ku sami abinda kuka roqa) masana suka ce gabas ne da kogin Jordan wanda shi ne yake da dausayin da za a iya duk wadannan shuke-shuken, kuma dai shi ne kusa da Tekun Lut AS wato inda mutanen Shu'aib AS suka rayu, Allah SW ya halakar da su ne a " Yaumuz zilla" saboda saba masa da suka yi, sai Shu'aibu AS da 'yan mutane qalilan wadanda suka yi imani suka kubuta, wadannan mutanen su ne ke riqe da muslunci suka hadu da mutanen Musa AS wato banu Isra'ila suka zauna anan Madayan muslunci ya ci gaba da jagoranci.
.
Ga alama zaman banu Isra'ila a Madyan ya dan dauki lokaci, qila ma shekaru, don anan ne qissar saniya ta faru, wace aka kawo ta a suratul Baqara, kuma anan din dai Annabi Musa ya hau tekun tsakiya wanda ake kira da Turanci (Mediterranean) har ya je inda tekun ya hadu da na Atalanta (wato Atlantic ocean) shi ne ake kiran wurin da Larabci "Majma'ul bahrain" ya yi tafiyar kilomitoci sama da dubu biyu da dari uku (2,300km) a kwale-kwale idan miqewa ce ta tsaki kai tsaye, wanda hakan zai yi matuqar wahala, kenan akwai yuwuwar kaiwa har kilomita 4,000 ma kafin ya kai tekun Atalanta, wannan tafiyar ba qarama ba ce, ko a jirgin ruwa ne mai inji a yau ka yi irin wannan tafiyar jikinka zai yi dumi, Qur'ani ya hakaito mana abubuwan da suka faru a hanya.
.
To bayan wannan ne Musa AS ya gaya musu cewa inda aka yi musu alqawarin zuwa fa bigire ne mai tsarki wato Palestine ba wannan garin na Madyan ba, sun zauna anan na dan lokaci ne, idan suka huta hankulansu suka dawo sai su fara neman inda aka yi musu alqawarin su koma da zama, amma abin takaici da suka je can sai suka fara neman dalilin da zai hana su shiga don su dawo wurinsu na asali, {قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِنَّ فِيهَا قَوْمًا جَبَّارِينَ وَإِنَّا لَنْ نَدْخُلَهَا حَتَّىٰ يَخْرُجُوا مِنْهَا فَإِنْ يَخْرُجُوا مِنْهَا فَإِنَّا دَاخِلُونَ}.
.
Suka ce "Musa akwai mugayen mutane a ciki mu kam ba za mu taba shiga ba sai sun bar ta, in za su bar ta to ko za mu shiga) Ma'ida22, a bayyane yake ba sa son shiga qasar ne amma ta ya 'yan qasa za su bar qasarsu gaba daya don ku ku zauna a ciki? Kenan banu Isra'ila sun zo Palestine dama akwai mutane. Shikenan Annabi Musa AS ya nada musu wakilai 12 wadanda za su riqa jagorancinsu, komai nasu ana raba shi ne gwargwadon wadannan gidajen guda 12.
.
Yanzu dai sun sani cewa wannan wurin da suke ba shi ne tabbataccen wurin da za su zauna ba dole sai sun nemo shi, Allah SW ya sauqaqe musu qarqashin jagorancin Musa AS amma suka qi shiga, to bayan ya koma ga Allah SW suka yi ta neman wurin amma ya gagara musu na tsawon shekara 40, Allah SW ya ladabtar da su ne, tsawon wannan lokacin ba annabci, sai dai Attaura da Musa AS ya bari a hannun manyansu su 12, ba su yi dace da wurin ba sai da suka tuba muslincibya karbi jagoranci.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)