MU’UTAZILANCI A TAƘAICE.

*MU’UTAZILANCI A TAƘAICE.*


*Mu’utazilanci* wata aƙida ce karkatacciya, wacce ta fanɗare daga tafarkin magabata. Ana danganta asalinta da wasu mutane irin su *Ja’adu Ɗan Dirham* da *Jahamu Ɗan Safwan* da su *Bishiru Al-Marrisiy.* Sai *Wasil Ɗan Aɗa'u;* wanda ake kallonsa a matsayin mutumin da ya kafa wannan aƙida ta mu’utazilanci tun bayan ƙauracewar da ya yi daga barin makarantar Al-Hasanul Basariy.

Akwai kuma malamai daga baya da alƙalai da suka yi fice a wajen yayata tafarkin Mu'utazila irin su *Jahiz* da *Alƙali AbdulJabbar* da *Ibn Abi Du'ad* da *Nazzam* da *Abu Ali Aljubba’iy* da *Zamakhshariy* da ire-irensu.

Hakanan kuma akwai sarakuna musamman na daular Abbasiyyah guda uku *(Ma'amun, Mu'utasim da Wasiƙ)* waɗanda suka shahara a tarihance a matsayin manyan masu bin tafarkin mu’utazilanci da kare shi a hukumance. 

Mu’utazila suna da wasu ƙa'idoji waɗanda suke gina addininsu akai. Ƙa’idojin guda biyar sune:

1. Tauheed: a wajensu yana nufin kore dukkan siffofin Allah waɗanda suke cewa wai tsarkake Allah ya lazimta lallai a kore su.

2. Adalci: adalci a wajensu shine ƙaryata cewa Allah (SWT) shi ya halicci ayyukan bayi.

3. Al’wa’adu Wal Wa'eed: shine zartar da hukuncin makoma ga mutane. Ta fuskar cewa dole ne Allah ya sanya wanda yai aikin kirki a aljanna. Dole ne kuma ya azabtar da wanda yai aikin banza.

4. Manzila Bainal Manzilataini: sun ƙirƙiro makoma ta uku, ita ce wata rugar-tsakani wacce suka ce anan za a dawwamar da masu laifukan da ayyukansu suka yi kan-kan-kan tsakanin alheri da sharri.

5. Umurni da Ƙyaƙƙyawa da Hani ga Mummuna: wannan kuma ƙuduri ne na tawaye da yaƙar shugabanni da yin fito-na-fito da masu mulki a bisa saɓanin tafarkin magabata na ƙwarai.

A wajen Mu’utazila, wadannan qa'idojin kamar rukunnai ne. Baya ga haka, Mu'utazila sun shahara da aƙidu masu zuwa:

- Musun yuwuwar ganin Allah a lahira.
- Musun ceto da nau’o'insa.
- Cewa Alquran halitta ne ba maganar Allah ba ne.
- Kore siffofin Allah al-khabariyya.
- Girmama al’amarin hankali da ɗaura shi a saman sharia.
- Murɗe ma’anar ayoyin Al-Ƙur'ani da suka saɓa wa irin hankalinsu.
- Tunkuɗe hadisan da suka saɓa wa hankalinsu komai ingancinsu.
- Raina magabata cikin sahabbai da tabi'ai da tuhumar su da ƙauyanci ko rashin aiki da hankali.
- Tunkuɗe hadisai ahad.
- Sukar malaman hadisi tun daga cikin sahabbai da tabi'ai har na bayansu.
- Fito-na-fito da mafi yawan abubuwan da akwai ijma'i akan su na aƙida ko manhaji.
- Ƙaryata tasirin sihiri da bokanci da shigar aljani jikin ɗan adam da ire-iren su na labaran gaibu.
- Karyata dawowar Annabi Isa (AS).

Allah ya sa mu dace.
Post a Comment (0)