KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 14

KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 14
.


Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa 
.
ƘA'IDOJIN ISAR DA SAƘONNI A MUSULUNCI
Akwai abubuwan da suka wajaba Musulmi ya yi la'akari da su wajen fahimtar manufar isar da saƙonni ko yaɗa labarai tsakanin al'umma, bisa mahangar addinin musulunci, kaɗan daga cikin waɗannan ƙa'idoji kuwa sun haɗa da:
.
1. Duk abin da mutum zai yi a doron ƙasa, na maganar fatar baki ne ko kuma aikin gaɓoɓi, wajibi ne ya aika wannan aiki tare da sanya shi bisa sikelin manufar halitattar ɗan'adam tare da neman yardar Allah, wajen gudanar da irin wannan aiki, na magana ne ko na gangar jiki. Watau aikin da ɗan'adam zai yi, ya kasance ya sanya shi a kan ma'aunin dokokin Allah, waɗanda Ubangiji ya tanada don bayinSa ya yi riƙo da su a matsayin hanyar bauta maSa.
.
Wajibi ne mutum ya gina maganganu da salon isar da saƙonni bisa babban jigon da musulunci ya ɗora mu a kansa na yaɗa alheri da gusar da ɓarna. Haka kuma mu kiyaye muhimmiyar ƙa'idar nan ta umurni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna. Don haka ana buƙatar dukkan bayanan da mutum zai yaɗa, su kasance sun dace da manufar kyawawan ayyuka da rusa munana cikin ɗaukacin mu'amala da zamantakewar al'umma.
.
3. Ana buƙatar manufar isar da saƙonni da yaɗa labarai tsakanin Musulmi ta kasance an gina ta ne bisa maslahar al'umma. Wannan ya ƙunshi kiyaye darajar shugabanci tsakanin al'umma, girmama wanda Musulunci ya buƙaci a girmama shi a dukkan rukunonin rayuwa; mutumta juna da kuma kyautata mu'amala ga kowa, sannan kuma da kaucewa keta mutumci da alfarmar abokin mu'amala. A ba da fifiko wajen yaɗa ayyukan alherai da ɗa'a, kuna a kiyaye yaɗa ɓarna da saɓon Allah. A rufa asirin juna, da kaucewa tozarci, da ƙazafi, da yarfe da tona asiri a tsakanin al'umma.
.
4. A kula da ƙarfafa manufar tsoron Allah da yin abu dominSa wajen isar da saƙonni da yaɗa labarai a tsakanin al'umma. Tsoron Allah a ɓangaren isar da saƙo zai sanya mutum yin takatsantsan wajen abin da zai isar ga al'umma, kuma zai sanya shi sanya rariya don tace duk abin da ya iso gare shi da kau da kai bisa abin da yake na ɓarna da saɓon Allah, ko na shiga haƙƙin ɗan'uwansa Musulmi ko ma wanda ba Musulmi ba, kuma tsoron Allah zai sanya mutum ya yi tunanin ranar da za a tsai da shi gaban Allah don yi masa hisabi bisa dukkan ayyukansa da maganganunsa a gaban Allah.
.
Komai za mu yi na yaɗa saƙonni a tsakaninmu, ya kasance don taimakawa ci gaban addininmu ne da maslahar rayuwarmu, amma ba don yaɗa ɓarna ko saɓon Allah ba. Allah (S.W.T) Ya ce:
وتعاونوا على البر والتقوى، ولا تعاونوا على الإثم والعدوان، واتقوا الله، إن الله شديد العقاب.                                   
".........Kuma ku taimaki juna a kan aikin ƙwarai da taƙawa, kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zalunci, kuma ku bi Allah da taƙawa, lallai ne Allah mai tsananin uƙuba ne.


Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)