KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 15

KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 15
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa 
.


ƘA'IDOJIN ISAR DA SAƘONNI A MUSULUNCI
5. Akwai buƙatar kiyaye amana wajen isar da saƙonni da yaɗa maganganu tsakanin al'umma kamar yadda Musulunci ya hore mu. Mu zama masu adalci da tsaida amana a tsakaninmu, kuma kada soyayya ko ƙiyayyar wani ta rinjaye mu wajen ƙirƙirar ƙarya da cin zarafi, ko tozarta wani. Wajibi ne mai isar da saƙo ko yaɗa labarai ya ajiye kowace ƙwarya a gurbinta, ba tare da nuna son rai ba, kuma ya kiyaye wajen tabbatar da sahihancin abin da zai faɗa, domin kada ya nemi karkatar da gaskiya don son rai ko biyan buƙatarsa ta duniya.
.
Za mu iya fahimtar muhimmancin hakan bisa isharar da Allah Ya yi wa bayinSa Muminai a cikin Alƙur'ani mai girma:
ياأيها الذين آمنوا كونوا قوامين لله شهداء بالقسط ولا يجرمنكم شنئان قوم على ألا تعدلوا اعدلوا هو أقرب للتقوى واتقوا الله إن الله خبير بما تعملون.                                
"Ya ku waɗanda suka yi Imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci, kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan ba za ku yi adalci ba, ku yi adalci, shi ne mafi kusa da taƙawa, kuma ku bi Allah da taƙawa, lallai Allah masani ne ga abin da kuke aikatawa". (Suratul Ma'ida: 8).
.
6. Kada mutum ya riƙa yaɗa sirrikansa na zamantakewar iyali ko sirrin ɗan'uwansa Musulmi ga sauran jama'a. Ka tuna, da zarar ka sami wani bayani, kuma ka yaɗa shi ta waɗannan kafofi, to ba ka da sauran iko wajen kankara ko sarrafar da abin da ka yaɗa, kuma ko da daga bisani ka yi tunanin share bayanan, duk wanda ya ga ko ya karanta waɗannan saƙonnin ya gama da kai, domin saƙon da ka isar ya kai gare shi, kuma yana da damar adana shi ko ya sake shi ta duk hanyar da ya ga dama.
.
Idan saƙonni na saɓon Allah ne da ƙetare iyaka, share shi kawai daga kafofin sadarwa ba zai gamsar da kai ba, sai ka tuba ka nemi gafarar Allah, don yaɗa ɓarnar da ka yi. Haka kuma sai ka nemi afuwa ga duk wanda saƙon ya cutar da shi, ko ka shiga haƙƙinsa.
.
7. Mu kiyaye waɗanda za mu yi mu'amala da su a kafofin sadarwa da sada zumunta, kuma mu sani aboki na ƙwarai a rayuwa babbar ni'ima ce, don haka mu zaɓi na ƙwarai, hatta cikin mu'amalar wannan kafa ta sadarwa ta zamani. Ga wasu tsokaci daga magabata a kan muhimmancin aboki na ƙwarai:
.
• Umar Bin Khaɗɗab (R.A) yana cewa: "Mafi girman ni'ima a duniya bayan imani shi ne, aboki na ƙwarai".
• Imamu Shafi'i yana cewa: "Aboki na ƙwarai yana da wuyar samu, in ka samu ka riƙe shi, don yana da saurin kuɓucewa".
• Immau Hasanul Basari yana cewa: "Aboki na ƙwarai mai nagarta ya fi iyalina a gare ni, don shi ne mai taimakona a duniyata da lahirata, kuma yana fifiita buƙatata a kan tasa buƙatar".
.
.

Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)