SHIN ZAN IYA BAWA DANA ZAKKA ?

SHIN ZAN IYA BAWA DANA ZAKKA ?


Tambaya :
Mutum yana da dansa, kuma dansa yana da iyali amma mai karamin karfi ne, to ya halatta ka bashi zakka? Allah ya karawa malam lafiya.

          Amsa :
To dan'uwa malamai suna cewa : duk wanda in ka mutu zai ci gadonka, to ba za ka ba shi zakka ba, ka ga kuwa Da yana cin gado a kowanne hali.
Sannan duk wanda ciyar da shi ya wajaba akanka, to ba za ka ba shi zakka ba, ya waja ba ga Uba ya ciyar da dansa, in dai talaka ne.
Duba Al-mugni (2/269) 

Saidai wasu malaman sun tafi akan cewa : ya halatta ya bawa dansa zakka don ya biya bashin da yake kansa, saboda biya masa bashi, ba wajibi ba ne akansa. Duba : Al-iktiyaraat din Ibnu-taimiyya shafi na : 104

Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa
2\7\2015

*MIFTAHUL ILMI*

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)