SIFFOFIN MIJI NA GARI 01SIFFOFIN MIJI NA GARI

Darasi na farko (1)

Kulluma ana ta wa'azi da nasiha akan yanda mace
zaka mallake mijinta da siffofin mace tagari da mata na kwarai,amma da wuya kaji ana magana akan abinda namiji ya kamata ya aikata dan farantama matarsa musulinci addini ne mai cike da adalci gaba daya,kowa yana da hakki akan dan uwansa.

1-Ka gyara bakinka saboda jin dadin kiss ga
matarka da sauran ibadar aure

Daga Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa;
"Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya shiga gidansa yana farawane da yin Aswaki"
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ .

2-Kariqa sanya turare mai dadi dan ka farantawa matarka,sannan kayi mata kwalliya kamar yanda kake so itama tayi maka

Daga Ibn Abbas ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ yana cewa;
"Ina so nayi kwalliya dan matata kamar yanda nake so tayi kwalliya sabo dani"
@ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ.

3-Kariqa karin matarka da suna mai dadi wanda
yake dauke da girmamawa da yabawa dan faranta mata rai

Manzon Allah ﷺ ya kasance yana cewa Nana A'isha;YÃ Ã'ISH ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺶ 
(ga Mala'ika Jibrilu nan yana yi maki sallama)
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.

To kaima ana so ka riqa yiwa matarka hakan dan
nuna soyayya da faranta mata rai.

Kuma Manzon Allah ﷺ ya kasance yana cewa Nana A'isha;
( ﻳﺎ ﺣﻤﻴﺮﺍﺀ YÃ HUMAIRA'U) 
@ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 818/7

ﻳﺎ ﺣﻤﻴﺮﺍﺀ;
Yana nufin yar budurwa kyakkyawa fara mai kyawun hali da dhabi'i.
Sau nawa ka taba fadawa matarka hakan?? Ko tun
tana amarya??

4-Kada ka riqa kiran matarka da sunanta
directly,ka sanya mata alkunya kamar maman wane da dai sauransu

Daga Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa;
"Nace ya Manzon Allah,kowace matarka tana da alkunya ta suna in banda ni kadai,sai ya sanya min alkunya yake kirana da"-
(Ummu Abdillahi)
@ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 255/1.

Kai ka sanyawa matarka alkunya saboda koyi da
sunnar Annabi ﷺ,ko kai baka da sunna wajan
kyautatama matarka?? Sunnar ka kadai itace gemu da dage wando da aswaki?? Mabiyin Sunnah na gaskiya shine wanda yake bin sunnar Manzon Allah ﷺ baki daya a kowane bangare.

5-Kada ka kyamaci mataka baki daya kariqa kallon kyautatawar da takeyi maka sai ka yafe mata laifinta

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
(Da ďaya mai imani baya kyamatar matarsa mai imani,idan ya kyamaci wani halinta to zai yabeta a wadansu halaye masu yawa)
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.

6-Gogewa matarka hawayen kuka tare da
rarrashinta dan nuna soyayya da kauna

Daga Anas ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ , yana cewa:
"Safiyya ta kasance tare da Manzon Allah ﷺ acikin bulaguro,kuma ya kasance ranar girkintane,sai rakuminta yaqi sauri har taji ba dadi,sai Manzon Allah ﷺ ya sameta tana kuka,tana cewa ka dorani
akan rakumi marar sauri,sai Manzon Allah ﷺ ya sanya hannuwansa yana goge mata hawaye yana rarrashinta yana sanyata tayi shiru"
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ.

Ahlussunnah shine koyi da Manzon Allah ﷺ
akowane bangare na rayuwarsa hatta mu'amalarsa da iyalinsa,to yana yine irin na Manzon Allah ﷺ,ko
baiyi duka ba to ya kwatanta.

    Allah ne mafi sani

Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)