TA YI BAKANCE, AMMA TA KASA CIKAWA, YAYA ZA TA YI?

TA YI BAKANCE, AMMA TA KASA CIKAWA, YAYA ZA TA YI?
:


*TAMBAYA*❓
:
Malam wata mace ce ta yi bakance za ta yi azumin Annabi Dawud, wato yau ta yi azumi gobe ta sha, amma kuma yanzu ta yi aure ta kasa, ya ya kamata ta yi ? shin akwai mafita ?_
:
*AMSA*👇
:
To dan'uwa Bakance makaruhi ne, haramun ne a wajan wasu malaman, saboda Annabi s.aw yana cewa : *"Bakance ba ya zuwa da alkairi"* kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1639. Saidai ya wajaba a cika bakance idan aka yi.

_Wasu daga cikin malaman hadisi sun ta fi akan cewa idan mutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai iya yin kaffarar rantsuwa, saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim a lamba ta: 1645 a sahihinsa, wanda Annabi s.a.w. yake cewa : *"Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce"*._

_Duba *Alminhaaj na Nawawy 4/269* A bisa abin da ya gabata za ki iya yin kaffarar rantsuwa wato: ciyar da miskinai goma, ko tufatar da su, ko kuma 'yanta kuyanga, idan babu hali, sai ayi azumi uku, kamar yadda yazo a suratul 
Ma'idah aya ta : 89 ._ 
Allah shine mafi sani.
.
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)